Dalilin da ya Sanya maTan hausawa ke tsufa da zaran sanyi Aure
DALILIN DA YA SANYA MATAN HAUSAWA KE TSUFA DA ZARAN SUNYI AURE: - Babbar matsalar mata a zamanin nan ita ce bakar kazanta da rashin kula da jikinsu matukar anyi aure. - Wannan mummunar dabi'ar kazantar na sa mace ta tsufa tare da ba miji hanyar neman matan banza a waje. - Dabi'ar kazanta na sa miji ya dinga kyamar matar shi ta yadda baya iya cin abincin da ta girka ballantana a kai ga kwanciyar aure. Sau da yawa auri saki ya fi ta'azzara tare da yawa a kasar hausawa. Haka zalika ganin karamar yarinya ta tsufa cikin shekara daya ko biyu bayan aure ya zama gama-gari. Yarinya budurwa tana yin aure, haihuwa daya zuwa biyu take yi ta zama wata uwar mata. A lokacin da take tashen budurcinta kuwa, zaka ganta yarinya sharaf mai aji, kwalliya, tsafta ga iya kame jikinta. Ba wani abu ke tsufar da matan ba da ya wuce kazanta. Mata da yawa bayan sunyi aure su kan yada makaman kwalliya, tsafta, gayu da kame jikinsu. Suna kuwa haihuwa daya, biyu zuwa uku suke tsufa kamar sun haifa mazan...